'Yan sanda na bincike kan nunawa Sterling wariyar launi
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tare da hadin gwiwar ‘yan sandan Birtaniya, sun kaddamar da bincike domin zakulo wadanda suka ci zarafin dan wasan Manchester City Raheem Sterling ta hanyar zagin nuna wariyar launi.
Wallafawa ranar:
Lamarin da ya auku ne a ranar Asabar da ta gabata, yayin wasan da Chelsea ta samu nasara kan Manchester City da kwallaye 2-0 a filin wasa na Stamford Bridge.
Cikin wani sako da ya aike ta kafar Instagram, Sterling ya zargi jaridun Birtaniya da bada gudunmawa, wajen karfafa laifukan cin zarafin ‘yan wasa bakake da dama, saboda yadda suke bada rahotanni ko bayanai kan akansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu