Isa ga babban shafi
Wasanni-Zakarun Turai

Brossia na fatan kar ta hadu da Liverpool a zagayen kungiyoyi 16

Kungiyar kwallon kafa ta Brossia Dortmund ta yi fatan kada ta hadu da takwararta Liverpool a zagayen kungiyoyi 16 da suka tsallake wasan Rukuni na cin kofin zakarun Turai.

Rahotanni sun ce kafin murmushin dan wasan a jiya bayan zura kwallo, rabon da a ga Murmushin Muhammad Salah tun bayan rashin nasarar su a hannun Real Madrid a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai bara.
Rahotanni sun ce kafin murmushin dan wasan a jiya bayan zura kwallo, rabon da a ga Murmushin Muhammad Salah tun bayan rashin nasarar su a hannun Real Madrid a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai bara. REUTERS/Jon Super
Talla

Bayan nasarar Liverpool da kwallo guda da banza wanda Muhammad Salah ya zura a ragar Napoli, Club din ya samu nasarar tsallakewa tare da PSG a rukunin C zuwa zagayen kungiyoyin 16.

Shugaban Brossia Dortmund Hans-Joachim Watzke a cikin bacin rai ya mayar da martinin ga dan jaridar da ya yi masa tambayar ko yana fatan haduwa da Liverpool a jadawalin UEFA na gaba inda ya ce sam bai kamata ya zama da Liverpool ne za su kara a nan gaba ba.

A litinin mai zuwa ne dai UEFA za ta fitar da jadawalin yadda karawar za ta gudana tsakanin kungiyoyin 16 wasan da zai kasance bugu daddai duk wadda aka yi nasara kan sa kai tsaye zai yi waje yayinda za a bar kungiyoyi 8 da za su tafi wasan gab da na kusa da na karshe.

Jadawalin na UEFA dai zai zamo cewa ba za a hada kungiyoyin da suka fito daga kasashe daya ba, haka zalika ba za a hada wadanda su ke a rukunin baya tare ba, wanda hakan ke nuna kungiyoyin biyu za su iya haduwa da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.