Isa ga babban shafi
Wasanni-Afrika

Salah ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika

Dan wasan gaba na Masar da ke taka leda a Liverpool Muhammad Salah ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara na Afrika, bayan doke takwarorinsa Medhi Benatia na Morocco da Kalidou Koulbaliy na Senegal da Sadio Mane Shima na Senegal da kuma Thomas Partey na Cote d voire.

Wannan dai ne karo na biyu da Muhammad Salah ke lashe kyautar ta gwarzon dan wasan Afrika.
Wannan dai ne karo na biyu da Muhammad Salah ke lashe kyautar ta gwarzon dan wasan Afrika. Liverpool
Talla

Muhammad Salah mai shekaru 26 ya yi nasarar ne bisa kwazon da ya nuna a wasannin Liverpool na kakar da ta gabata inda ya zura kwallaye 44 a wasa 52.

Cikin jawabansa na godiya bayan mika masa kyautar Salah ya ce ya yi matukar farin ciki da sake lashe kyautar kuma ya na fatan ya kara lashe ta a shekara mai zuwa.

Dan wasan wanda shi ne ake ganin a matsayin wanda ya kai kasarsa ga gasar cin kofin duniya bayan shafe shekaru 20 ba a ji duriyarta ba, kwallaye 2 kacal ya iya jefawa a raga cikin wasannin da Masar ta buga a Rasha inda aka yi waje da ita tun daga wasan rukuni-rukuni.

Haka zalika bayan rawar da ya taka a gasar Firimiya cikin kakar wasa ta 2018 a bangaren gasar cin kofin zakarun Turai ya kai Liverpool har wasan karshe wanda ta yi rashin nasara hannun Real Madrid da kwallaye 3 da 1.

Salah wanda ya samu kuri’u dubu dari 5 da 50 ya ce fatansa shi ne ganin ya daga wani kofi mai muhimmanci a Liverpool ko da dai kai tsaye dan wasan bai fito ya fadi kofin da ya ke harin lashewa ba, amma masana harkokin wasanni na ganin bazai wuce na Firimiya ko Zakarun Turai ba, la’akari da yadda ya ke kara hazaka a wannan kaka.

Muhammad Salah dai shi ne dan wasa na baya-bayan nan da ya taba lashe kyautar fiye da sau daya run bayan dan wasan Najeriya Jay-Jay Okocha wanda ya dau shekaru yana lashe kyautar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.