Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester United ta kori Mourinho daga bakin aiki

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sanar da korar Jose Mourinho bayan rashin katabus a wannan kaka musamman a gasar Firimiyar Ingila wadda za a iya cewa ya faro da kafar hagu.

A cewar Club din Korar Mourinho wadda zai haddasa musu asarar akalla Yuro miliyan 18 ya biyo bayan gaza samarwa Club din sauyi duk da yuro miliyan 400 da ya kashe wajen sayen ‘yan wasa 11.
A cewar Club din Korar Mourinho wadda zai haddasa musu asarar akalla Yuro miliyan 18 ya biyo bayan gaza samarwa Club din sauyi duk da yuro miliyan 400 da ya kashe wajen sayen ‘yan wasa 11. Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Mourinho dan Portugal mai shekaru 55 ya fara horar da United ne a watan Mayun 2016 inda ya kai ta ga lashe kofin League da na Europa, ko da dai a wanna kaka har yanzu tazarar maki 19 ne tsakaninsa da Liverpool da ke saman teburin Firimiya, haka zalika da kyar ya sha wajen kaiwa zagayen kungiyoyi 16 na gasar zakarun Turai.

A cewar Club din Korar Mourinho wadda zai haddasa musu asarar akalla Yuro miliyan 18 ya biyo bayan gaza samarwa Club din sauyi duk da yuro miliyan 400 da ya kashe wajen sayen ‘yan wasa 11.

Yanzu haka dai Club din ya sanar da mataki laluben Manajan wucin gadi da zai ja ragamar kungiyar zuwa wasansu da Cardiff Fc ranar 22 ga watan nan, yayinda kuma zai dauki sabon mai horarwa a kakar wasa mai kamawa.

Tuni dai masu sharhi ke ganin Club din na harin ko dai Zinedine Zidane ko Diego Simeone ko kuma Mauricio Pochettino don maye gurbin Mourinho wanda ya jagoranci United a wasanni 144 ya yi nasara a 84 canjaras a 32 ya kuma yi rashin nasara a 28 yayinda karkashin jagorancinsa Club din ya zura kwallaye 243 aka kuma zura masa 117.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.