rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni FIFA Kwallon Kafa Gasar Cin Kofin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Rabin al'ummar duniya sun kalli gasar cin kofin duniya ta 2018"

media
Hedikwatar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da ke birnin Zurich na kasar Switzerland. REUTERS/Arnd Wiegmann/Files

Hukumar kula da kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta ce mutane kusan biliyan 1 da miliyan 20 ne suka kalli wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta bana, da aka fafata tsakanin Faransa da Croatia a Rasha.


FIFA wadda ta bayyana haka a wannan Juma’a, ta ce a jimlace mutane biliyan 3 da miliyan 572 suka kalli jimillar wasannin gasar cikin kofin duniyar na tsawon akalla minti guda, tsakanin 14 ga watan Yuni zuwa 15 ga Yuli, ranar da aka kammala gasar.

FIFA ta kara da cewa bincikenta ya nuna cewa, mutane biliyan 3 da miliyan 40 sun kalli gasar cin kofin duniyar na tsawon akalla mintuna 3, yayin da mutane biliyan 2 da miliyan 49 suka kalli akalla mintuna 30 na wasannin gasar daban daban da aka fafata.

A cewar FIFA dukkan wasannin da aka fafata guda 64 yayin gasar ta bana, sun samu jimillar masu kallo daga sassan duniya akalla miliyan 191.

Wasan karshe kuwa tsakanin Faransa da Croatia, FIFA ta ce jimillar mutane miliyan 884 da dubu 37 suka shaida yadda fafatawar ta kaya.