Isa ga babban shafi
wasanni

Sociedad ta bai wa Real Madrid kashi a gida

Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid ta sha kashi a hannun Real Sociedad da ci 2-0 kuma aka karon farko kenan cikin shekaru 15 da Sociedad ke doke Madrid a gidanta, wato Santigo Bernabeu a gasar La Liga ta Spain.

Gareth Bale bai buga wasan da Real Madrid ta sha kashi a hannun Real Sociedad ba.
Gareth Bale bai buga wasan da Real Madrid ta sha kashi a hannun Real Sociedad ba. REUTERS/Susana Vera
Talla

Real Madrid ta kara tsundima cikin tsaka mai wuya a wasan na ranar Lahadi bayan da alkalin wasa ya bai wa Lucas Vazquez jan kati, abin da ya sa ta kammala fafatawar da ‘yan wasa 10.

Madrid ta yi wasan ne ba tare da dan wasan gabanta ba, wato Gareth Bale da ke fama da rauni a kafarsa , yayin da Isco ya shiga wasan daga baya.

Yanzu haka akwai tazarar maki 10 tsakanin Real Madrid da babbar abokiyar hamayyarta, wato Barcelona wadda ke jan ragamar teburin gasar ta La Liga.

A bangare guda, Lionel Messi ya jefa kwallonsa ta 399 a gasar La Liga bayan da suka doke Getafe da ci 2-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.