Isa ga babban shafi
Wasanni

Hazard ya fi karfin zama a Chelsea - Jenas

Tsohon dan wasan Tottenham Jermaine Jenas ya ce a halin yanzu kwarewa da kwazon dan wasan gaba na Chelsea Eden Hazard, ya fi karfin kungiyar tasa.

Dan wasan gaba na kungiyar Chelsea Eden Hazard.
Dan wasan gaba na kungiyar Chelsea Eden Hazard. Reuters / Stefan Wermuth Livepic
Talla

Jenas ya bayyana haka ne, yayin da yake tsokaci kan wasan kusa dana karshe na kofin Carabao da aka sani da Carlin a baya, wanda a ranar Talata Tottenham ta samu nasara kan Chelsea da 1-0.

Tsohon dan wasan na Tottenham, ya ce lokaci yayi da Hazard mai shekaru 28, zai rabu da Chelsea ya koma wata babbar kungiya a nahiyar ta Turai, saboda yadda kwarewar dan wasan ta girmi kungiyar tasa.

An dai jima ana alakanta Eden Hazard da rahotannin yana shirin sauya sheka daga Chelsea zuwa Real Madrid, zalika shi kansa dan wasan ya sha bayyana sha’awar komawa kungiyar ta Madrid, sai dai kawo yanzu hakan bai tabbata ba.

Yarjejeniyar Hazard da Chelsea za ta kare a shekarar 2020, kuma har yanzu bai sa hannu kan kara wa’adinta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.