Isa ga babban shafi
wasanni

Wasan Juventus da Milan ya haddasa rudani a Saudiya

A yayin da kungiyar kwallon kafa ta Juventus ke harin lashe kofinta na farko a cikin sabuwar shekarar 2019 a gasar Super Cup ta Italiya, ana ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya kan wasu batutuwa da dama da suka danganci fafatawar da AC Milan a gobe Laraba a birnin Jedda na Saudiya.

Hukumomin Saudiya sun takaita wa mata shiga filin wasan na Sarki Abdalla, in da za a kece raini tsakanin Juventus da AC Milan a wasan karshe na gasar Super Cup
Hukumomin Saudiya sun takaita wa mata shiga filin wasan na Sarki Abdalla, in da za a kece raini tsakanin Juventus da AC Milan a wasan karshe na gasar Super Cup (Foto: Reuters)
Talla

Amnesty International ta bukaci kungiyoyin biyu da su kaurace wa fafatawar a Saudiya saboda zargin da ake yi wa kasar na kisan dan jaridan nan Jamal Khashoggi, baya ga cewa, hukumomin Saudiya sun takaita wa mata samun tikitin shiga kallon wasan, in da suka ce, dole ne duk macen da za ta kalli wasan kai tsaye, ta sayi tikitin zama a bangaren masu iyali, umarnin da mataimakin Firaministan Italiya, Matteo Salvini ya yi watsi da shi.

A bangare guda, shugaban shirya gasar Serie A ta Italiya, Gaetano Micciche, ya kare matakinsu na yanke shawarar buga wasan a Saudiya, wadda ta kasance kasar Islama, in da yake cewa, hakan wani babban tarihi ne a gare su.

A karo na goma kenan da mahukuntan gasar Super Cup ke gudanar da wasan karshe na gasar a can wata kasa da ba Italiya ba. in da a baya-bayan nan aka gudanar da wasannin na karshe a kasashen Amurka da Canada da Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.