Isa ga babban shafi
Wasanni

Higuain zai koma Chelsea, Morata zai fice daga cikinta

Rahotanni daga kafafen yada labaran wasanni da dama a Turai, sun tabbatar da cewa, Chelsea tana gaf da kammala sayen dan wasan gaba na kungiyar AC Milan Gonzalo Higuain dan kasar Argentina.

Gonzalo Higuain dan kungiyar AC Milan da ke shirin komawa Chelsea.
Gonzalo Higuain dan kungiyar AC Milan da ke shirin komawa Chelsea. REUTERS/Daniele Mascolo
Talla

Higuain dai yana matsayin dan wasa ne na aro a kungiyar ta AC Milan, daga kungiyar Juventus.

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Chelsea da AC Milan, Higuain zai koma kungiyar ta Chelsea ne a matsayin aro na tsawon watanni 12, tare da zabin tabbatar da sayensa ko kara wa’adin zamansa tare da ita a matsayin na aro.

Sauyin shekar ta Higuain zai bashi damar sake haduwa da tsohon mai horar da shi Maurizio Sarri, wanda suka yi aiki tare a Napoli, a waccan lokacin kuma Higuain ya ci wa kungiyar kwallaye 36 kafin komawa Juventus kan cinikin euro miliyan 90.

Tuni dai kungiyar Chelsea ta shirya mikawa Atletico Madrid da ke Spain aron dan wasanta na gaba Alvaro Morata, a dalilin shirin zuwan Higuain daga kungiyar AC Milan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.