Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi ya roki masu aikin ceto su ci gaba da laluben jirgin Sala

Fitaccen dan wasan gaba na Argentina da ke taka leda a Barcelona Lionel Messi ya roki jami’an agajin da ke aikin lalauben jirgin Emiliano Sala su dawo da aikin laluben maimakon dakatarwar da suka yi a jiya, yana mai cewa har yanzu suna da kwarin gwiwar za a iya gano shi.

Dan wasan Argentina da ke taka leda a Nantes ta Faransa Emiliano Sala wanda Cardiff ta saya kan yuro miliyan 18 amma kafin kai wa Ingila jirginsa ya yi batan dabo.
Dan wasan Argentina da ke taka leda a Nantes ta Faransa Emiliano Sala wanda Cardiff ta saya kan yuro miliyan 18 amma kafin kai wa Ingila jirginsa ya yi batan dabo. REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Cikin wani sako da Messi ya wallafa a shafin Instagram, ya roki jami’an tsaron da su ci gaba da aikin tare dan neman magoya baya su ci gaba da addu’ar gano Sala dan shekaru 28 da Cardiff ta sayo daga Nantes ta Faransa kan yuro miliyan 18.

Kiran na Messi na zuwa bayan makamancinsa daga Mahaifin Sala da kuma sauran ‘yan wasa ciki har da Valentin Vada na Badu da Diego Roland na Leganes dukkaninsu kungiyoyin kwallon kafar Faransa.

Yanzu haka dai iyalai da ‘yan uwan Emiliano Sala sun ki amincewa da makokinsa bisa yakinin cewa tabbas ya na raye a wani waje da ban, inda suka bukaci Tsohon Club Emiliano, Nantes ya janye matakinsa na yunkurin makoki ga dan wasan da ya shirya gudanarwa cikin makon nan.

A bangare guda shi ma Captin din Nantes ya shaidawa dubban masoyan Sala da suka taru a filin wasan Club din kan su sanya a ran su Sala na raye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.