Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid ta doke Girona a gasar Copa del Rey

Sergio Ramos ya taimakawa kungiyarsa ta Real Madrid wajen lallasa Girona da 4-2, a wasan gasar Cope del Rey na Spain, ya jefa kwallaye 2 a ragar abokan hamayyarsu.

'Yan wasan Real Madrid yayin murna kan kwallon da Sergio Ramos ya jefa a ragar Girona, yayin wasan kwata final na gasar cin kofin Copa del Rey na kasar Spain.
'Yan wasan Real Madrid yayin murna kan kwallon da Sergio Ramos ya jefa a ragar Girona, yayin wasan kwata final na gasar cin kofin Copa del Rey na kasar Spain. Reuters
Talla

Dan wasan Sevilla Anthony Lozano ya soma jefa kwallo a ragar Madrid kafin daga bisani Ramos da Lucas Vazquez su ramawa kungiyar tasu.

Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema ya jefa kwallo ta 4, yayinda Alex Granell ya jefawa Sevilla kwallonta ta 2.

A halin yanzu Sergio Ramos ya ci wa kungiyarsa ta Madrid kwallaye 9 a dukkanin wasannin da ya buga mata, bayan soma kakar wasa ta bana.

Nasarar ta Real Madrid dai, za ta kara mata karfin gwiwar tunkarar manyan wasanni biyu da ke gabanta a watan Fabarairu, inda za ta kara da Atletico Madrid a gasar La Liga, yayinda a gasar zakarun nahiyar Turai kuma, za ta fafata da kungiyar Ajax.

A halin yanzu Real Madrid ta samu nasara a wasanni 4 daga cikin biyar da ta buga a baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.