Isa ga babban shafi
Wasanni

Neymar zai shafe makwanni da dama yana jinya

Dan wasan gaba na PSG kuma mafi tsada a duniyar kwallo a halin yanzu, Neymar, ya koma Faransa a ranar Alhamis, bayan da likitoci a Spain suka kammala gudanar gwaji kan raunin da ya samu a kafarsa ta dama.

Dan wasan gaba na kungiyar PSG, Neymar, a filin jiragen sama na Barcelona, yayin shirin komawa Faransa. 31/01/2019.
Dan wasan gaba na kungiyar PSG, Neymar, a filin jiragen sama na Barcelona, yayin shirin komawa Faransa. 31/01/2019. YouTube
Talla

Sai dai abin da ya dauki hankalin mutane shi ne yadda Neymar ke amfani da sanduna wajen dogarawa yayin tafiya, abinda ke nuni da cewa lallai raunin da ya samu babba ne.

A makon da ya gabata dan wasan ya samu rauni a kafarsa ta dama, yayin fafatawar PSG da Starsbourg a gasar cin kofin Faransa wato 'Coupe de France', hakan yasa Neymar ba zai samu damar buga wasannin biyu na PSG za ta fafata da Manchester United ba a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Likitocin da suka duba lafiyar kafar ta Neymar, sun ce dan wasan baya bukatar tiyata, sai dai tilas ya shafe makwanni 10 ba tare da sake buga kwallo ba, la’akari da cewa ya samu raunin ne a kafar da ya taba samun karaya cikin watan Fabarairu na shekarar bara, wanda ya tilasta masa jiyyar fiye da watanni 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.