Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta soma shirin rigakafi bayan rabuwa da Messi

Shugaban kungiyar Barcelona, Josep Maria Bartomeu, ya ce suna kan shirye-shirye ganin sun ci gaba da samun nasarori a wasanninsu, idan Messi yayi ritaya daga bugawa kungiyar wasa.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi.
Dan wasan Barcelona Lionel Messi. Sergio Perez/Reuters
Talla

Bartomeau wanda ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai, ya ce a bayyane take kungiyar ta Bacelona a shirye-shiryen rayuwa ba tare da Messi ba, idan aka yi la’akari da irin ‘yan wasan da suke saya a baya bayan nan, kamar Frenkie de Jong mai shekaru 21, da Barcelona da sayo daga kungiyar Ajax kan fam miliyan 65.

Messi wanda a yanzu shekaru biyu ya rage yarjejeniyarsa da Barcelona ta kare, a shekarar 2017, ya furta cewa yana gaf da cimma burinsa na ritaya daga kwallon kafa a gida.

Messi wanda ya kasance tare da Barcelona tun a shekarar 2005, ya ci wa kungiyar kwallaye 581 daga cikin wasanni 664 da ya buga mata.

Dan wasan mai shekaru 31, ya kuma taimakawa Barcelona wajen lashe kofunan La Liga 9, kofunan gasar zakarun Turai 4, da kuma kofunan gasar Copa del Rey 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.