Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester United ta koma ta 4 a Firimiyar Ingila

Likkafar Manchester United na ci gaba da dagawa a gasar Premier ta Ingila, bayan da kungiyar ta lallasa takwararta Fulham da kwallaye 3-0.

Tun bayan karbar ragamar jagorancin United da Ole Gunnar Solskjaer ya yi daga hannun Jose Mourinho, kungiyar ta samu nasara a wasanni 10, daga cikin jimillar wasanni 11
Tun bayan karbar ragamar jagorancin United da Ole Gunnar Solskjaer ya yi daga hannun Jose Mourinho, kungiyar ta samu nasara a wasanni 10, daga cikin jimillar wasanni 11 REUTERS/David Klein
Talla

Nasarar ta bai wa United damar komawa mataki na 4 a gasar ta Premier daga matsayi na 6 da ta ke kai a baya.

‘Yan wasan Manchester United Paul Pogba da Martial ne suka jefa kwallayen a ragar Fulham.

Karo na farko kenan da Manchester United ta samu nasara a jimillar wasanni 6 da ta fafata a gidan abokan karawarta, tun bayan irin bajintar da ta nuna a kakar wasa ta 2009 cikin watan Mayu.

Tun bayan karbar ragamar jagorancin United da Ole Gunnar Solskjaer ya yi daga hannun Jose Mourinho, kungiyar ta samu nasara a wasanni 10, daga cikin jimillar wasanni 11 da ta fafata.

Ranar Talata 12 ga watan Fabarairu, Manchester United za ta yi tattaki zuwa Faransa, domin fafata wasan zagayen farko tsakaninta da kungiyar PSG, a gasar zakaru nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.