rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Ingila Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Raunuka a kai da gadon baya suka haddasa mutuwar Sala - Likitoci

media
Emiliano Sala. REUTERS/Stephane Mahe

Binciken likitoci ya gano cewar sabon dan wasan Cardiff City da ya mutu a hadarin Jirgi Emiliano Sala, ya rasa ransa ne sakamakon raunukan da ya samu a kansa da kuma gadon baya.


A makon da ya gabata jamiā€™an ceto suka ciro gawar Sala daga baruguzan jirgin da yayi hadari a ruwan dake tsakanin Faransa da Ingila, sai dai har yanzu ba a gano gawar matukin jirgin David Ibbotson da kuma wani mutum guda dake tare da su ba.

A ranar Litinin gwarzon dan kwallon kafa na duniya ajin matasa, Kylian Mbappe ya bada tallafin euro dubu 27,000 ga gidauniyar da aka kafa domin neman David Ibbotson, wanda a makon da ya gabata aka kawo karshen aikin nemansa saboda yankewar kudaden gudanarwa da kuma rashin kyawun yanayi.