Anya Liverpool za ta doke Bayern Munich kuwa?
Yau ne Liverpool za ta barje gumi da Bayern Munich a Gasar Zakarun Nahiyar Turai, kuma a karo na biyu kenan tun shekarar 1981 da kungiyoyin biyu za su kara da juna a wata babbar gasar Turai.
Wallafawa ranar:
To sai dai ayar tambayar da masana harkar kwallon kafa ke digawa ita ce, anya Liverpool ta shirya kece raini da Bayern Munich kuwa, wadda ta lashe kofin Bundesliga sau shida a jere a baya-baya nan?
Sannan kuma akalla ta kai matakin wasan dab da na karshe a Gasar Zakaun Turai sau biyar a kakanni shida da suka gabata.
Kazalika, Bayern Munich din na cikin kungiyoyi biyar da ba a doke su ba a matakin rukuni a Gasar Zakarun Turai a bana.
Koda yake alkaluma sun nuna cewa, babu wata kungiya da ta doke Liverpool a wasanni 19 da ta yi a jere a Anfield, wato gidanta da za a yi karawar ta yau.
Ita ma Barcelona za ta kai ruwa rana da Lyon a Gasar ta Zakarun Turai, yayin da dan wasan baya na Barcelona, Gerard Pique ke cewa za su fuskanci matsala a fafatawar muddin ba su gyara wasu matsaloli ba.
Pique ya ce, matukar suka yi kasa a guiwa wajen rarraba kwallon cikin gaggawa ko kuma rasa karsashin mamaye wasan, to lallai za su samu koma-baya a karawarsu da Lyon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu