Isa ga babban shafi
wasanni

'Yan wasan Chelsea sun rikice a gaban Manchester United

Mai horar da Chelsea, Maurizio Sarri ya ce, ‘yan wasansa sun buga rikitaccen wasan kwallon kafa a fafatawar da Manchester United ta casa su da ci 2-0 a gasar cin kofin FA a Stamford Bridge.

Kocin Chelsea, Maurizio Sarri
Kocin Chelsea, Maurizio Sarri reuters
Talla

Yanzu haka Manchester United ta samu nasarar tsallakwa matakin wasan dab da na kusan karshe, wato Kwata Fainal, yayin da kocin na Chelsea ya dada tsindima cikin tsaka mai wuya. Koda dai ya ce, ba zai damu idan kungiyar ta kore shi.

Tsohon dan wasan Chelsea, Chris Sutton ya ce, za a kori Sarri kafin wasan da kungiyar za ta yi nan gaba.

Magoya bayan Chelsea sun yi wa Sarri ba’a saboda sauye-sauyen da ya yi a fafatawar ta ranar Litinin, in da kuma suka bukaci a nada Frank Lampard domin ci gaba da horar da kungiyar.

Kazalika, magoya bayan na Chelsea sun hada baki da takwarorinsu na Manchester United wajen rera wake-waken ganin an sallami Sarri daga mukaminsa na kocin kungiyar.

A cewar Sarri, ‘yan wasansa sun buga rikitacciyar kwallo bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.