Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester City ta lashe kofin gasar Carabao

Manchester City sun samu nasarar lashe gasar cin kofin Carabao, bayan da a jiya Lahadi suka samu nasarar doke Chelsea a wasan karshe da suka fafata.

'Yan wasan Manchester City, bayan samun nasarar lashe kofin gasar Carabao.
'Yan wasan Manchester City, bayan samun nasarar lashe kofin gasar Carabao. Reuters
Talla

Kafin a karkare wasan, sai da aka buga jimillar mintuna 120, wato mintuna 90 kamar yadda aka saba da kuma Karin lokacin mintuna 30, ba tare da kowace kkungiya tasamu nasarar cin kwallo ko da daya ba.

A zagayen bugun daga kai sai mai tsaron gida ne Manchester City ta doke Chelsea da kwallaye 4-3.

Rasa damar lashe gasar cin kofin Carabao ga Chelsea ya zo ne makwanni 2, bayan kaye mafi muni da kungiyar ta taba fuskanta cikin shekaru 28, a hannun Manchester City da ta lallasa ta da kwallaye 6-0 a fafatawarsu ta gasar Premier.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.