Isa ga babban shafi
Wasanni

Magoya bayan Madrid na fatan yiwa kungiyar sabon zubi

Masu bibiyar lamurran da ke wakana a duniyar kwallon kafa, sun zura idanu don ganin irin matakan da hukumar gudanarwar Real Madrid za ta dauka, wajen yi wa kungiyar garambawul.

'Yan wasan Real Madrid Karim Benzema, Gareth Bale da kuma Luka Modiric, yayin jim kadan bayan lallasa su da kungiyar Ajax ta yi da kwallaye 4-1 a gasar Zakarun Turai.
'Yan wasan Real Madrid Karim Benzema, Gareth Bale da kuma Luka Modiric, yayin jim kadan bayan lallasa su da kungiyar Ajax ta yi da kwallaye 4-1 a gasar Zakarun Turai. SIPA USA/PA Images
Talla

Sauraron yiwa Madrid garambawul dai ya biyo bayan yadda Kungiyar Ajax ta lallasata da kwallaye 4-1 yayin fafatwarsu a jiya Talata a gasar zakarun Turai, matakin kungiyoyi 16, lamarin da ya sa kungiyar ta Madrid ficewa daga gasar, baya yin rashin nasara da kwallaye 5-3 a hannun Ajax idan aka hada wasannin biyun da suka fafata.

Manyan sauye-sauyen da magoya bayan Real Madrid da sauran masu sharhi ke dako, sun hada da saida tsaffin ‘yan wasa da kuma sayo sabbi , sai kuma uwa uba sauya mai horarwa.

Har yanzu dai kocin kungiyar na yanzu Santiago Solari na da sauran lokaci a yarjejeniyar da ya kulla da ita, wadda za ta kare a shekarar 2021, sai dai hakan ba shi ke nuna cewa zai ci gaba da rike matsayin nasa ba, la’akari da barin manyan kofuna 3 da Real Madrid ta yi cikin mako daya.

Tun kafin zuwan wannan lokaci dai ake bayyana kwakkwaran zaton cewa tsohon kocin Manchester United, wanda kuma ya taba horar da Real Madrid din a baya, Jose Mourinho zai sake karbe ragamar horar da kungiyar, matakin da ake sa ran zai tabbata kowane lokaci daga yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.