rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Spain Italiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Marcelo ya bi sahun Ronaldo wajen komawa Juventus daga Real Madrid

media
Dan wasan Real Madrid Marcelo da ya amince da komawa Juventus google.com

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta amince da ka’idojin cinikin dan wasan gaba na Real Madrid, Marcelo kan yuro miliyan 12, akan kwantiragin shekaru 4 wato nan da shekarar 2023.


Mercelo wanda a baya-bayan nan ke fuskantar bancawa daga Solari manajan Real Madrid dama ba tun yanzu ba ake rade-raden ya na shirin hadewa da abokinsa Cristiano Ronaldo wanda shima ya koma Juventus din a bara.

Yanzu haka dai kowanne lokaci daga yau Juma’a Mercelo na iya tunkarar Turin don haduwa da sabbin abokanan wasansa na Juventus.

Mercelo wanda ya shafe fiye da shekaru 10 a Real Madrid ya dage kofuna gasa daban-daban har 20 ciki har da na zakarun Turai 4 kuma dan wasa ne da ya ke iya buga gefe da kuma baya wanda ake ganin shi ne ya maye gurbin Roberto Carlos.

Dai dai lokacin da Real Madrid ke fuskantar koma baya a fagen tamaula bayan da ta gaza cike gibin da Ronaldo ya bari a Club din ana ganin rashin zakakurin dan wasa kamar Marcelo babban kalubale ne gareta.