rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Argentina Gasar Cin Kofin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Messi ya janye haramcin wakiltar Argentina da ya kakabawa kansa

media
Lionel Messi. REUTERS/Marcos Brindicci

Dan wasan Argentina Lionel Messi zai koma bugawa kasarsa wasa, bayan kawo karshen yajin shiga tawagar kwallon kafa ta kasar da yayi bayan da Faransa ta fitar da su daga gasar cin kofin duniya a mataki ko zagayen kasashe 16.


Tuni dai kocin tawagar kwallon Argentina, Lionel Scaloni, ya sanya Messi cikin ‘yan wasan da za su fafata da kasashen Venezuela da Morocco a wasannin sada zumunci cikin wannan wata.

A gefe guda, Angel Di Maria na kungiyar PSG da shi ma aka shafe lokaci mai tsawo bai bayyana a tawagar kwallon kafar ta Argentina ba, a wannan karon ya samu shiga.

Sai dai babu manyan ‘yan wasan kasar ta Argentina cikin wannan tawaga, da suka hada da Sergio Aguero da ke Manchester City, Mauro Icardi na Inter Milan da kuma Gonzalo Higuain da ke Chelsea, duk kuwa da kokarin da ake ganin suna yi a kungiyoyinsu.