Isa ga babban shafi
Wasanni

Roma ta kori kocinta

Kungiyar AS Roma ta kori kocinta Eusebio Di Francesco, sa’o’i bayan fitar da ita daga gasar zakarun turai da FC Porto ta yi a ranar Laraba.

Eusebio Di Francesco, kocin da kungiyar AS Roma ta kora.
Eusebio Di Francesco, kocin da kungiyar AS Roma ta kora. REUTERS/Sergei Karpukhin/File Photo
Talla

Shugaban kungiyar ta Roma James Pallota ne ya sanar da matakin, bayan wani taron gaggawa masu ruwa da tsaki a kungiyar da ya jagoranta.

Di Francesco ya karbi ragamar horar da Roma a watan Yunin 2017, har zuwa jiya Alhamis da kungiyar ta sallame shi, duk da cewa ‘yan wasanta sun bayyana goyon bayansu gare shi kamar yadda kaftin dinsu Danele De Rossi ya bayyana.

A halin yanzu tsohon kocin Leicester City Claudio Ranieri ake sa ran zai karbi jagorancin horar da kungiyar.

Ranieri dai ya taba horar da kungiyar ta AS Roma daga watan Satumba na shekarar 2009 zuwa Fabarairu a 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.