Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona da Liverpool sun yi nasarar zuwa mataki na gaba a gasar Zakarun Turai

A ci gaba da gasar neman kofin zakarun Turai, an samu karin kungiyoyi biyu da suka wuce zuwa zagayen Quarter-Final bayan da suka yi nasara a wasannin da suka buga cikin daren laraba, wato Liverpool da kuma Barcelona.

Dan wasan Lyon Jason Denayer na neman kwallo daga kafar dan wasan Barcelonais Luis Suarez,
Dan wasan Lyon Jason Denayer na neman kwallo daga kafar dan wasan Barcelonais Luis Suarez, Susana Vera/Reuters
Talla

Liverpool ta yi nasara a gidan Bayern Munich 3-1 a filin wasa 3-1 na Alianz Arena, abin da ya bai wa Liverpool damar shiga sahun kungiyoyi 8 sau biyu kenan a jere.

Dan wasan Liverpool Sadio Mane ya zura kwallayen biyu a wasan, yayin da Van Dijk ya yi nasarar zura kwallo daya.

Wannan dai ba karamar nasaba ba ce ga ‘yan wasan kasar Ingila, domin kuwa daga cikin kungiyoyin kwallo kafa 8 da suka rage a gasar ta zakarun Turai, 4 sun fito ne daga kasar.

Wannan ne dai karon farko da za a shiga zangon kungiyoyi 8 ba tare da Bayern Munich ba, tun bayan da ta fuskanci irin wannan koma-baya a kakar wasannin 2011 lokacin da ta sha kashi a hannun Inter Milan ta Italia.

Barcelona ta lallasa Lyon

A cikin daren laraba, an fafata tsakanin Barcelona da Lyon, inda aka tashin wasan Barcelona ce ke da nasara 5-1, kuma Lionel Messi ne ya zura kwallaye biyu.

To sai dai an dan samu cece-kuce sakamakon wani bugun fenirati da aka bai wa Barcelona a wasan na jiya, domin sai da aka yi amfani da kemarar taimaka wa alkali kafin tabbatar da hakan a minti na 16 da fara wannan wasa.

A zagayen farkon dai an tashi tanjaras ne ba tare da wani ya zura kwallo a raga ba tsakanin Lyon da kuma Barcelona.

A yanzu dai kungiyoyin da suka yi saura a gasar ta Zakarun Turai sun hada da Barcelona, Liverpool, Manchester City, Tottenham, Manchester United, Juventus, Ajax da kuma Porto, kuma a gobe juma’a ne hukumar kwallon kafar Turai za ta fitar da jadawali dangane da yadda wadannan kungiyoyi za su kara a matakin Quarter Final

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.