Isa ga babban shafi
Wasanni-kwallon kafa

Jadawalin wasannin gab da na kusa da na karshe na cin kofin zakarun Turai

Hukumar UEFA ta fitar da jadawalin wasannin gab da na kusa da na karshe na cin kofin zakarun Turai da za a fafata tsakanin kungiyoyi 8, inda a wannan karon ya kama dole kungiyoyin firimiya 2 su kara da juna, la’akari da yadda kungiyoyin Ingila har 4 suka samu gurbin tsallakewa zuwa wasannin.

A wannan karon dai kungiyoyin Ingila 4 ne suka samu zuwa wannan mataki wanda ke matsayin sabo a tarihin gasar
A wannan karon dai kungiyoyin Ingila 4 ne suka samu zuwa wannan mataki wanda ke matsayin sabo a tarihin gasar Reuters
Talla

Jadawalin na UEFA dai ya nuna cewa Barcelona za ta kara da Manchester United yayinda Manchester City za ta kara da Tottenham.

A bangare guda Juventus wadda ta fitar da Atletico Madrid bayan kwallaye 3 da Ronaldo ya zura a raga ranar Talata, za ta kara da Ajax wadda ta fitar da Real Madrid mai rike da kambun har sau 3 a jere, wadda kuma shekaru 16 kenan rabonta ma da fita daga wasannin rukuni-rukuni na gasar.

Ita ma dai Liverpool kungiya ta 4 cikin jerin kungiyoyin kwallon kafar Ingila da suka samu gurbi a gasar za ta kara da Porto ta Netherland, wadda ko a bara ma dai kungiyoyin biyu sun kara a irin wannan mataki inda Liverpool ta yi waje da Porto da jumullar kwallaye 5 da banza a gida da waje.

Tuni dai masu sharhi kan wasanni ke ci gaba da tsokaci inda su ke ganin wasu kungiyoyin am basu tubus-tubus yayinda wasu kuma aka fara hango musu fuskantar shan kaye mai muni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.