rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Ingila Premier League

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Salon wasan da Solskjaer ke bi na tattare da ganganci - Rashford

media
Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford. REUTERS/Peter Powell

Dan wasan gaba na Manchester United Marcos Rashford, ya bayyana salon da sabon kocinsu Ole Gunnar Solskjaer ke basu umarnin bi a wasanni, a matsayin salo ko tsari mai tattare da hadarin gaske.


A cewar Rashford, Solskjaer na basu umarnin maida hankalinsu kacokan wajen samun nasarar jefa kwallaye a raga a kowane hali, ko da kuwa kwallon ba ta hannunsu a dai dai wannan lokacin.

Rashford ya kara da bayyana cewa Solskjaer na basu umarnin cewa yayin da suke kokarin tsare gida lokacin fafata wasa, a dai dai lokacin kuma su kasafta kwakwalensu zuwa tunanin, yadda za su kai samamen da zai basu damar antaya kwallo a ragar abokan karawa da zarar sun amshe ta.

Tun bayan karbar ragamar horar da Manchester United daga hannun Mourinho, da Solskjaer ya samu nasara a wasanni 14 daga cikin jimillar 19 da kungiyar ta fafata, ta hanyar amfani da salon maida hankali wajen kai hare-haren jefa kwallo a raga, abinda wasu ke kallo a matsayin "Ganganci wai dukan ganga da lauje".