rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Olympic

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Libya ta lallasa Najeriya a wasan neman tikitin zuwa gasar Olympics

media
Najeriya na fuskantar barazanar rasa damar halartar gasar Olympics a bangaren kwallon kafa. REUTERS/Nigel Roddis

Libya ta lallasa Najeriya da kwallaye 2-0 a zagayen farko na wasan kwallon kafa da suka fafata, na neman cancantar halartar gasar Olympics da kasar Japan za ta karbi bakunci.


A ranar Litinin mai zuwa, kasashen za su sake fafatawa a zagaye na 2, inda najeriya za ta karbi bakuncin Libyan a babban filin wasan jihar Delta da ke Asaba.

Hukumar lura da wasannin Olympics, ta takaita wasannin kwallon kafa neman cancantar halartar gasar ce a tsakanin ‘yan wasan da ke kasa da shekaru 23.

Sauran wasannin neman cancantar da aka buga a ranar Laraba 20 ga watan Maris, 2019, tsakanin kasashen nahiyar Afrika sun kunshi, wasan da Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, ta lallasa Morocco da 2-0 a birnin Kinshasa.

Sudan ma lallasa Kenya ta yi da kwallaye 2-0 a birnin Omdurman, yayinda Guinea ta samu nasara kan Senegal da  2-1.

Zambia tayi tattaki zuwa Malawi ta kuma samu nasara da 1-0.

Wasa tsakanin Burundi da Congo Brazzaville da aka fafata a birnin Bujumbura kuwa an tashi 0-0.

Kasashe uku ne za su wakilci Nahiyar Afrika a fagen kwallon kafa, yayin gasar ta Olympics za ta gudana a Tokyo babban birnin kasar Japan.