rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Ingila Montenegro

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An nuna wa 'yan wasan Ingila wariyar launin fata

media
Tawagar Ingila ta ce, za ta shigar da kara a gaban hukumar kwallon kafar Turai kan nuna wa 'yan wasanta wariyar launin fata FIFA.COM

‘Yan wasan Ingila, Raheem Sterling da Callum Hudson Odoi sun yi tir da matsalar nuna wariyar launin fata a wasan da Ingilar ta lallasa Montenegro da ci 5-1 a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin kasashen Turai ta 2020.


A yayin wasan na ranar Litinin, an yi ta rera wakar nuna wariyar launin fata da zummar muzanta wa wasu daga cikin ‘yan wasan na Ingila da suka hada da Danny Rose.

Kocin tawagar Ingila, Gareth Southgate ya ce, za su shigar da kara a gaban Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai kan wannan batu.

Southgate y ace, ba za a amince da irin wannan dabi’ar ba, yayinda ya jaddada cewa, da kunnensa, ya ji ana zagin Danny Rose.

Shi ma Hudson Odoi ya ce, da kunnesa, ya ji magoya bayan Montenegro na kukan birrai, yana mai cewa, bai kamata a rika samun irin wannan dabi’ar ba domin kuwa, dukkan mu daya muke.