rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Olympic Tseren Gudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ba zan sha maganin da zai rage karfina ba - Semenya

media
Caster Semenya, shahararriyar 'yar tseren gudu daga Afrika ta Kudu. REUTERS

Shahararriyar ‘yar tseren gudu ta kasar Afrika ta Kudu, Caster Semenya, ta kafe kan matsayinta na kin amincewa da bukatar shan magunguna da za su rage tsabar karfi da zubin da take da shi tamkar namiji.


A watannin da suka gabata Semenya ta garzaya kotu domin, tilastawa hukumar shirya wasannin motsa jiki ta duniya, ba ta damar ci gaba da fafatawa a wasannin motsa jiki da hallitarta, ba tare da rage mata karfi, ko dora ta kan magungunan da za su rage kirar karfi ta namiji da take da shi ba.

Gasar karshe da Semenya ta lashe, ita ce ta gudun mita 800 a babban birnin Qatar, wato Doha, inda ta kammala gudun mita 800 din cikin minti daya, da dakika 54.

Yayin gasar dai Semenya ta baiwa Francine Niyonsaba, da ke biye da ita a matsayin ta biyu, tazarar mitoci 20, saboda karfin gudun da take da shi.