rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Premier League

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kompany ya cirewa Manchester City kitse daga wuta

media
Dan wasan Manchester City Vincent Kompany, yayin murnar kwallon tarihi da ya jefa a ragar Leicester City, tare da takwarorinsa, Sterling da Aguero. 6/5/2019. REUTERS/Phil Noble

Manchester City ta sake karbe gurbin matsayi na 1 teburin gasar Premier a jiya litinin, bayan da ta tsallake rijiya da baya a wasan da ta samu nasara kan Leicester da 1-0.


Dan wasan City Vincent Kompany ne ya ci kwallon tilo, wadda ta kasance irinta ta farko da ya ci wa kungiyar tasa daga wajen yadi na 18, a lokacin da ya rage mintuna 20 a tashi daga wasa.

Yayin tsokaci kan kwallon bayan tashi daga wasa, Kompany ya ce duk da cewa bai ci kwallo ko guda ba a kakar wasa ta bana sai a wasan na jiya, ya dade yana ji a jikinsa cewa akwai wata bajinta, ko ceton da zai yiwa kungiyar tasa a lokacin da take kishirwar hakan.

A halin yanzu maki daya ne tsakanin Manchester City da Liverpool a gasar ta Premier, inda City ke matsayi na daya da maki 95, Liverpool na biye da maki 94, sai kuma Chelsea mai maki 71.

A karshen teburin gasar kuwa Fulham ce ta 19 da maki 26, sai kuma ta karshe Huddersfield mai maki 15 kacal, da ta zamewa Manchester United kadangaren bakin tulu.