Isa ga babban shafi
Wasanni

Za a yi karon battar karfe tsakanin Liverpool da Barcelona

Yau za a yi karon battar karfe tsakanin Liverpool da Barcelona a zagaye na biyu na wasan kusa da na karshen gasar zakarun turai.

Wasu daga cikin 'yan wasan da kungiyoyin Liverpool da Barcelona.
Wasu daga cikin 'yan wasan da kungiyoyin Liverpool da Barcelona. Reuters
Talla

Sai dai Liverpool za ta buga wasan a yau talata ba tare da dan wasanta Muhammad Salah ba.

Salah ba zai haska a wasan na yau ba, saboda raunin da ya samu a wasan Premier na ranar Asabar da ta gabata, wanda suka samu nasara akan Newcastle da kwallaye 3-2.

Bayaga Salah, wani karin dan wasan gaban na kungiyar ta Liverpool Roberto Firmino, ba zai buga wasan na yau ba, shi ma saboda raunin da ya samu.

Yayin tsokaci kan karawar ta yau, kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce ba abu ne mai sauki ba, su fitar da Barcelona daga gasar zakarun Turai, la’akari da rashin yan wasan nasa biyu, to sai dai ba za su fidda rai ba, muddin suna da, yan wasa 11 a kan fili.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.