rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Liverpool ta zare wa Barcelona laka a Anfield

media
'Yan wasan Liverpool na murnar zura kwallaye a ragar Barcelona Phil Noble/Reuters

Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool ta tsallaka zuwan matakin wasan karshe a gasar zakarun Turai bayan da ta doke Barcelona da jumullar kwallaye 4-3.


Liverpool ta bayar da mamaki matuka a Anfiled lura da cewa, ta farke dukkanin kwallaye ukun da Barcelona ta zura mata a makon jiya a Camp Nou, sannan kuma ta kara ta hudu.

Kocin Liverpool, Jurgen Kloop, ya bayyana nasarasu akan Barcelona a matsayin wani abin al’ajabi, musamman idan aka yi la’akari cewa, sun yi wasan ne ba tare da Mohamed Salah da Roberto Firmino ba da aka hutar da su saboda rashin lafiya.

A cewar Kloop, zai ci gaba da tunawa da wannan nasarar har iya karshen rayuwarasa.

Kocin ya kara da cewa, murna ta lullube shi, in da kuma ‘yan wasansa suka zubar da hawaye bayan samun wannan gagarumar nasarar.

Liverpool dai ta maimata abinda ta yi wa AC Milan a shekarar 2005 a birnin Santanbul, lokacin da ta lashe kofin gasar a karo na biyar.

Yanzu haka Liverpool za ta hadu da kodai Ajax ko kuma Tottenham a wasan karshe na gasar ta zakarun Turai a ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa a birnin Madrid.

Idan anjima ne za a kece raini tsakanin Ajax da Tottenham, yayinda ake  ganin watakila Ajax ta samu nasara, kuma da ma tana da kwallo guda da ta zura a ragar Tottanham a haduwarsu ta farko.