rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Gasar Zakarun Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Lokaci yayi da Liverpool za ta sayi Messi - Johnson

media
Kaftin din Barcelona Lionel Messi, bayan da Liverpool ta fitar da su daga gasar Zakarun Turai a filin wasanta na Anfield. Phil Noble/Reuters

Tsohon gwarzon dan wasan Liverpool, Craig Johnson, ya shawarci kungiyar da ta yi yunkurin sayen gwarzo kuma kaftin din Barcelona Lionel Messi.


Johnson, ya ce darajar Liverpool a halin yanzu ta kai matsayin soma tunkarar manyan ‘yan wasa da nufin sayensu, la’akari da lallasa Barcelona da kungiyar ta yi da kwallaye 4-0 a zagaye na 2, na wasan kusa da na karshen gasar zakarun Turai.

A jiya Talata Barcelona ta barar da damar kaiwa zagayen karshe na gasar Zakarun Turai, a wasan da suka fafata da Liverpool duk da cewa, a zagayen farko na wasan kusa da na karshen, Barcelona ta samu nasara a Spain da 3-0.

Shi kuwa tsohon dan wasan Manchester United Rio Ferdinand shawartar ‘yan wasan Barcelona yayi da cewa, daga yanzu ya kamata su rika mutunta filin wasan Liverpool na Anfield, musamman idan suka sake komawa filin wani lokaci a gaba.