rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Spain La liga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

La Liga ta samu riba mafi girma a shekara daya

media
Kudaden shigar da gasar ta La Liga ke samu a shekara guda ya karu da kusan kashi 21. REUTERS/Albert Gea

Gasar kwallon kafa ta La Liga da ke Spain, ta bayyana samun adadin kudaden shiga mafi yawa da ta samu cikin kakar wasa guda, a tarihin kafuwarta.


Akalumman dai sun shafi kakar wasa ta 2017/2018, inda gasar kwallon kafar ta Spain ta ce kudaden shigar da ta samu a kakar wasan ya kai euro biliyan 4 da miliyan 479, sabanin Euro biliyan 3 da miliyan 600 da ta samu a kakar 2016/2017.

Adadin ya nuna cewa, yawan kudaden shigar da gasar ta La Liga ke samu a shekara guda ya karu da kusan kashi 21.

A gefe guda kuma, rahoton wani bincike da aka gudanar ya bayyana cewa, gasar La Liga ta samar da guraben ayyukan ni ga mutane akalla dubu 185,000, da kuma baiwa gwamnatin Spain gudunmawar kudaden haraji da yawansu ya haura sama da euro biliyan 4 a kowace shekara.