Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool da Tottenham za su kara a wasan karshe na gasar zakarun Turai

Kungiyoyin kwallon kafa na Liverpool da Tottenham za su kara da juna a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai da zai gudana a Madrid a farkon wata mai kamawa, bayan da Tottenham ta yi nasarar lallasa Ajax ta Netherland da kwallaye 3 da 2, a jiya, yayinda ita kuma Liverpool ta lallasa Barcelona da kwallaye 4 babu ko daya a shekaran jiya Talata.

Wani wasa tsakanin Liverpool da Tottenham karkashin gasar Firimiya
Wani wasa tsakanin Liverpool da Tottenham karkashin gasar Firimiya Reuters/Paul Childs
Talla

Tottenham dai wannan ne zai zamo mata karon farko da za ta taba buga was an karshe na cin kofin zakarun turai, yayinda ita kuma Liverpool ko a bara ta kai matakin amma Real Madrid ta koro ta da kwallaye 3 da 1.

Tuni dai masana wasanni suka fara sharhi kan wasan na watan gobe, wanda ake ganin ba mai sauki ba ne la'akari da yadda kungiyoyin biyu ke kusan matsayin karfi guda, inda ko a wasanninsu na Firimiya su kan yi canjaras a lokuta da dama.

Wasan dai tsakanin Liverpool da Tottenham zai zamo irinsa na 3 da kungiyoyin Ingila biyu za su kara da juna a wasan karshe na wata babbar gasa a nahiyar Turai, wato tun bayan was an karshe na cin kofin UEFA tsakanin Tottenham da Wolves a shekarar 1972 da kuma was an karshe na cin kofin zakarun turai a shekarar 2008 tsakanin Man United da Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.