rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hankalin Liverpool ya koma kan kofin zakarun Turai

media
Magoya bayan Liverpool sun yi takaicin gaza lashe kofin firimiya na Ingila Reuters/Carl Recine

Kocin Liverpool, Jurgen Kloop ya kalubalanci ‘yan wasansa da su yi amfani da radadin rashin lashe kofin gasar firimiya ta Ingila a matsayin wani kaimi da zai taimaka musu lashe kofin zakarun Turai a bana.


Liverpool ta kammala gasar firimiya ta bana da banbacin maki guda tsakaninta da Manchester City wadda ta sake lashe kofin a bana.

Liverpool ta kammala gasar ne da maki 97, yayinda Manchester City ta kammala da maki 98.

Kodayake Liverpool ta samu nasara a karawar da ta yi da Wolves da ci 2-0, amma hakan bai yi tasiri ba ko kadan, lura da cewa, Manchester City ta doke Brighton da ci 4-1, abinda ya haramta wa Liverpool din daga kofin firimiya a karon farko cikin shekaru 29.

Yanzu haka Liverpool ta mayar da hankalinta kan lashe kofin gasar zakarun Turai, in da za ta kara da Tottenham a wasan karshe a birnin Madrid a ranar 1 ga watan gobe.

A bangare guda, kocin Manchester City, Pep Guadiola ya bayyana cewa, kare kambin gasar firimiyar Ingila a wannan shekara, shi ne lokaci mafi wahala a gare shi a tarinhinsa na kwallon kafa.

A cewar kocin, sake lashe kofin bai zo musu da sauki ba, musamman ganin yadda suka barje gumi a wasanni 14 da suka samu nasara a jere.

Guardiola dai ya lashe kofin gasar La Liga sau uku a jere a lokacin da yake jagorancin Barcelona a Spain, sannan kuma ya sake lashe kofin Bundesliga sau uku a jere a lokacin da yake Bayern Munich ta Jamus.

A yanzu kocin na fatan a badi ya sake lashe kofin firimiyar Ingila, wanda hakan zai kasance sau uku kenan a jere da zai lashe kofin.