Isa ga babban shafi
Wasanni

Griezmann zai yi ban-kwana da Atletico Madrid

Dan wasan gaba na Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya ce, zai raba gari da kungiyar a karshen wannan kakar bayan shafe shekaru biyar yana murza mata tamaula.

Antoine Griezmann ya ci wa Atletico Madrid kwallaye 133 a wasanni 256.
Antoine Griezmann ya ci wa Atletico Madrid kwallaye 133 a wasanni 256. OLIVIER MORIN / AFP
Talla

Griezmann da ya lashe kofin duniya a cikin tawagar Faransa, ya kulla sabon kwantiragi da Atletico Madrid har na shekaru biyar, amma a yanzu ya tsayar da shawarar barin kungiyar da zaran ya buga mata wasan da za ta yi da Levante a ranar Asabar mai zuwa a gasar La Liga.

Rahotanni na cewa, kungiyar kwallon kafa ta Barcelona za ta biya Euro miliyan 120 domin karbe dan wasan. Kodayake a bara ya yi watsi da tayin da Barcelona ta yi masa.

Dan wasan ya zura kwallaye 133 a wasanni 256 da ya buga wa Atletico Madrid tun bayan komawarsa kungiyar daga Real Sociedad a shekarar 2014, yayin da ya lashe kofunan Europa da Spanish Supar cup da kuma UEFA Super Cup.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.