rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa La liga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Real Madrid za ta yi tankade da rairaya

media
Kocin kungiyar Real Madrid Zinedine Zidane. © REUTERS/Susana Vera

Rahotanni daga Spain sun ce akwai yiwuwar Real Madrid za ta saida ‘yan wasanta da dama bayan kammala karkare kakar wasa ta bana.


Matakin ya zo ne a dai dai lokacin da kocin kungiyar Zinaden Zidane ke shirin aiwatar da yin gagarumin garambawul ga kungiyar, domin maido da karsashin da ta rasa a baya.

‘Yan wasan da ake sa ran Real Madrid za ta saida sun hada da Gareth Bale, James Rodriguez wanda ke zaman aro a Bayern Munich, Jesus Vallejo, Mateo Kovacic, Dani Ceballos, Marcos llorente da kuma Lucas Vazquez.

Sauran yan wasan kuma sun kunshi mai tsaron ragar kungiyar ta Real Madrid Keylor Navas, Brahim Diaz Mariano Diaz sai kuma Oscar Rodriguez.