rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Seria A Italiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Seria A

media
Cristiano Ronaldo yayin murnar jefa kwallo a ragar Atletico Madrid. 12/3/2019. Massimo Pinca/Reuters

Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon shekara na gasar Seria A da ke Italiya.


Ronaldo ya lashe kyautar ne a shekararsa ta farko da ya soma wasa a gasar ta Seria A bayan barin Real Madrid zuwa Juventus kan cinikin euro miliyan 100 a shekarar bara.

Hakan na nufin Kaftin din Portugal da ya ciwa Juventus jimillar kwallaye 21 a kakar wasa ta bana, ya lashe kyautar ta gwarzon dan wasa a kasashen Ingila, Spain da kuma Italiya.