Isa ga babban shafi
Wasanni

De Gea ya yanke shawarar rabuwa da United

Mai tsaron ragar Manchester United, David De Gea ya yanke shawarar rabuwa da kungiyar kafin kakar wasa ta badi.

Mai tsaron ragar Manchester United, David De Gea.
Mai tsaron ragar Manchester United, David De Gea. Reuters / Lee Smith Livepic
Talla

Matakin na De Gea ya kawo karshen muhawarar da wasu ke yi kan makomarsa a kungiyar, la’akari da sukar da yake fuskanta a baya bayan nan, musamman daga magoya bayan kungiyar, saboda wasu kura-kurai da ya rika yi, a wasannin da suka fafata.

A halin yanzu rahotanni sun ce tuni mai tsaron ragar na United ya yi watsi da tayin kara wa’adin yarjejeniyar da kungiyar ta mika masa, bayan dakatar da tattaunawa da wakilanta, kan tsawaita yarjejeniyar da za ta kare a 2020.

An dai shafe wasu watanni ana alakanta De Gea da komawa kungiyar Real Madrid.

A gefe guda kuma rahotanni sun ce a makon da ya gabata, kungiyar Manchester United ta mikawa Ajax tayin sayen mai tsaron ragarta Andre Onana domin maye David De Gea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.