rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Seria A Italiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sarri ya amince da tayin komawa Juventus

media
Kocin Chelsea Maurizio Sarri. REUTERS/Hannah McKay

Mai horas da kungiyar Chelsea Maurizio Sarri, ya amince da tayin komawa Juventus don maiye gurbin kocinta Massimiliano Allegri, bayan kammala karkare kakar wasa ta bana, inda Chelsea za ta fafata da Arsenal a wasan karshe na gasar Europa.


Juventus ta samu nasarar cimma yarjejeniya da Sarri, bayan da Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ki amincewa da tayin Juventus din na karbar aikin horas da yan wasanta, ko da yake daga bisani itama Juventus ta musanta rahotannin da suke ce ta tuntubi Guardiola.

A baya dai, kungiyar ta Juventus ta yi kokarin cimma yarjejeniya da tsohon kocin Chelsea Antonio Conte ko kuma tsohon kocin Manchester United Jose Mourinho, amma hakarta ta gaza cimma ruwa.

Sai dai a yanzu tuni ciniki ya fada tsakanin Maurizio Sarri da kungiyar ta Juventus, wanda za ta rika biyansa euro miliyan 6 da dubu 100 a shekara, a karkashin yarjejeniyar da za ta shafe shekaru 3.