Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta yi nasarar zuwa zagaye na gaba a gasar U20

Najeria ta yi nasarar zuwa zagaya na gaba a gasar neman kofin Duniya na matasa ‘yan kasa da shekaru ashirin (U20) da ke gudana yanzu haka a kasar Poland, bayan da aka tashi kunnen doki 1-1 a karawar da Najeriya ta yi cikin daren jiya alhamis da kasar Ukraine.

Tambarin hukumar kwallon kafar duniyar FIFA a Zurich, Switzerland 26satumbar 2017. REUTERS/Arnd Wiegmann/File Photo
Tambarin hukumar kwallon kafar duniyar FIFA a Zurich, Switzerland 26satumbar 2017. REUTERS/Arnd Wiegmann/File Photo REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Wasan dai ya kasance mai zafi, saboda har aka shiga mintuna na 51 Ukraine ce ke da nasara a kan Najeriya ci 1 da nema, duk da cewa ‘yan wasan Najeriya sun samu bugun finariti amma kuma Muhammed Tijjani ya barar.

Najeryar ta sake samun wani finariti karo na biyu, inda a wannan karon Tijjanin ya yi nasaarar zura kwallo a ragar Ukraine, abin da ya sa aka tashi wasan 1-1.

Wasanni da aka buga a gasar ta ‘yan kasa da shekaru 20 sun hada da :

-Amurka wadda ta lallasa Qatar 1-0

-Najeriya ta yi kunnen doki da Ukraine 1-1

-Norway ta doke Honduras 12-0

-Sai Uraguay da ta zura wa New Zealand kwallaye 2-0

A wannan juma’a za a ci gaba da wasannin, inda Mali da za ta fafata da Faransa, Saudiyya za ta hadu ne da Panama, Argentina ta hadu ta Koriya ta Arewa, yayin da Afrika ta Kudu za ta fafata da Portigal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.