rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa League 1 Paris Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Neymar ya musanta zargin aikata laifin fyade

media
Dan wasan kungiyar PSG Neymar. AFP /Lionel Bonaventure

Tauraron kwallon kafar Brazil, kuma na kungiyar PSG, Neymar, ya musanta zargin da wata mata ke masa, na yi mata fyade a Faransa.


Bayanan da jami’an ‘yan sandan Brazil suka fitar, ya ce matar ta kai musu rahoton cewa cin zarafin ya auku ne a wani Otal da ke babban birnin kasar ta Faransa wato Paris.

Matar wadda yan sandan basu bayyana sunan ta ba, ta ce, ta soma haduwa da Neymar ne ta shafin Instagram, daga bisani kuam suka shirya haduwa a Paris, dan wasan kuma ya biya mata kudin jirgi.

Matar ta kara da cewa bayan haduwarsu ne Neymar ya ci zarafinta, yayinda yake cikin maye kamar yadda ta yi ikirari.

Sai dai cikin jawabin da yayi na tsawon mintuna 7 ta shafinsa na Instagram, Neymar ya yi watsi da zargin wanda ya bayyana shi da yunkuri na bata masa suna.