rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Brazil

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Neymar ba zai buga gasar Copa America ba saboda rauni

media
Dan wasan Brazil, Neymar Foto: Reuters

Dan wasan gaba na Brazil, ba zai samu fafatawa a gasar nahiyar Kudancin Amurka ta COPA AMERCA ba sakamakon raunin da ya ji a idon sawu a wasan sada zumunta da Brazil ta kara da Qatar.


Hukumar kwallon kafar Brazil ta tabbar da wannan labari bayan Neymar ya fice daga filin wasa a daren Laraba yana hawaye.

Wata sanarwar da hukumar ta fitar na cewa : ‘’bayan Neymar ya murgude idon sawun kafarsa a wasan daren Laraba da Qatar, an mai gwaje gwaje kuma an tabbatar da fashewar wata jijiya a idon sawunsa’’.

Tauraron dan wasan na Paris Saint Germaine ya fara wasan ne a gaba tare da Richarlison da Gabriel Jesus, yayin da Brazil ta fara shirye shiryen buga gasar ta Copa America.

Bayan wani dan wasan Qatar ya rafke shi ne ya zame wa shi Neymar dole ya bar filin wasan a minti na 21 da fara wasa.

Ranar 14 ga wannan watan ne Brazil zata kara a wasan farko na gasar da Bolivia.