rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa FIFA

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Madrid ta amince ta sayi Hazard kan dala miliyan 165

media
Dan wasan Chelsea, Eden Hazard REUTERS/Hannah Mckay

Real Madrid ta amince ta sayi dan wasan Chelsea, Eden Hazard kan kudin da ya kai dala miliyan 165 bayan an shafe kwananki ana tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu.


Real Madrid ta amince ta sayi dan wasan Chelsea, Eden Hazard kan kudin da ya kai dala miliyan 165 bayan an shafe kwananki ana tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu.

Hazard ne dai babban kamun da Real Madrid ke sa ran yi a kokarin da take na sake gina tawaga mai karfi don tunkarar wasannin ta na cikin gida da ma na nahiyar Turai, kuma cikin ‘yan kwanaki wannan ciniki zai kammala.

Bayan an shafe kwanaki ana musayar yawu tsakanin Real da Chelsea, a karshen wannan mako hukumomin kungiyoyin biyu suka cimma yarjejeniya.

Hazard zai bar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ne bayan shekaru 7 yana taka mata leda, inda ya lashe kofunan gasar Firimiyar Ingila biyu, kofin gasar Turai na Europa biyu FA daya da League Cup daya.

Ya ci kwallaye biyu a wasan karshe na gasar Europa tsakanin Chelsea da Arsenal a watan da ya gabata a birnin Baku, bayan wasan ne ma ya furta cewa yana ganin zamansa a Stamford Bridge ya zo karshe.

Shekara daya da ta wuce Hazard yake ta fatan komawa Real Madrid amma Chelsea ta yi ta yin kafar ungulu a batun,kafin daga bisani ta amince.