Isa ga babban shafi
Wasanni

Amunike zai ci gaba da horar da 'yan wasan Tanzania

Hukumar Kwallon Kafar Tanzania ta bayyana cewa, Emmanuel Amunike zai ci gaba da aikin horar da tawagar kwallon kafar kasar duk da cewa ya gaza kai kasar ga gaci a gasar cin kofin Afrika da ke gudana a Masar.

Kocin Tanzania Emmanuel Amunike
Kocin Tanzania Emmanuel Amunike Reuters
Talla

Tanzania ta samu gurbi a wannan gasar ce bayan ta shafe tsawon shekaru 39 raban da a dama da ita a gasar, yayinda a wannan karo ta sha kashi a dukkanin wasanninta guda uku da ta buga a matakin rukuni.

Tanzania ta fada  a rukunin C, inda aka hada ta da kasashen Senegal da Algeria da Kenya.

Darektan horar da wasanni na hukumar kwallon kafar Tanzania, Ammy Ninje, ya shaida wa manema labara a birnin Alkahira cewa, Amunike ya taka rawa wajen dawo da martabar kasar a fannin kwallon kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.