rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Seria A Italiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buffon ya koma tsohuwar kungiyarsa

media
Gianluigi Buffon. Massimo Pinca/Reuters

Tsohon mai tsaron ragar kasar Italiya Gianluigi Buffon, ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Juventus akan yarjejeniyar buga mata wasa tsawon shekara daya.


Komen na Buffon ya zo ne bayan da ya shafe kakar wasa guda tare da kungiyar PSG, da ya koma gareta a ranar 19 ga watan Mayu na 2018, wadda ya buga mata wasanni 25 a tsawon zamansa tare da ita.

Buffon mai shekaru 41, ya shafe shekaru 17 tare da Juventus da ya yiwa kome a halin yanzu.

Mai tsaron ragar, ya kafa tarihin zama dan wasan da yafi wakiltar kasarsa Italiya da adadin buga mata wasanni 176.