Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Halep da Djokovic sun lashe kofunan gasar tennis ta Wimbledon

Ranar lahadi Novak Djokovic dan kasar Serbia ya lashe kofin gasar Wimbledon, bayan doke abokin karawarsa Roger Federer na Switzerland, a wasan karshen daya kafa tarihin zama mafi tsawon lokaci da aka dauka ana fafatawa.

Zakarun gasar kwallon tennis da Wimbledon a 2019, Simona Halep da Novak Djokovic.
Zakarun gasar kwallon tennis da Wimbledon a 2019, Simona Halep da Novak Djokovic. Reuters/File Photo
Talla

An dai shafe sa’o’i ko awanni 4 da mintuna 57 kafin kammala wasan karshen na gasar tennis din ta Wimbledon a birnin London.

Nasarar da Djokovic ya samu ta bashi damar kafa tarihin zama dan wasan tennis na farko cikin shekaru 71, da ya samu nasarar farfadowa daga barzanar rashin nasarar da yake fuskanta ya kuma lashe kofin gasar ta Wimbledon.

A bangaren mata kuwa, ranar asabar Simona Halep ta Romania ta lashe kofin a gasar tennis din ta Wimbledon.

Halep ta kafa tarihin zama yar kasar Romania ta farko da ta lashe gasar bayan doke ba Amurkiya Serena Williams da ci 6-2 da kuma 6-2

Karo na farko kenan da Serena Williams ke rashin nasara sau uku jere da juna a wasannin karshe na manyan wasannin tennis na duniya.

A watan Satumban shekarar 2017, Serena Wiiliams ta dawo fagen wasan kwallon tennis tana a matsayin mai jego, watanni 4 kacal bayan haihuwar da tayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.