Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Juventus ta karkare cinikin De Ligt daga Ajax

Dan wasan gaba na Holland da ke taka leda a Ajax Matthijis De Ligt ya isa Juventus don fara yi masa gwaje-gwajen lafiya a gobe Laraba, bayan kammala cininkinsa tsakanin Ajax da Juventus a jiya Litinin.

Dan wasan Ajax da ke kokarin komawa Juventus Matthijs de Ligt
Dan wasan Ajax da ke kokarin komawa Juventus Matthijs de Ligt Olaf Kraak / ANP / AFP
Talla

De Ligt dai ya amince da rattaba hannu kan kwantiragin shekaru 5 da Juventus wanda farashinsa ya kai yuro miliyan 75 kan yarjejeniyar biyansa yuro miliyan 12 duk shekara a matsayin albashi.

De Ligt mai shekaru 19 wanda shi ne Kaptin din Ajax a wasanni 117 da ya bashi damar zura kwallaye 13, tauraruwarsa ta haska ne matuka bayan nasarar kai Club din ga wasannin gab da na karshe na cin kofin zakarun Turai bayan shekaru 22.

Cikin manyan kungiyoyin kwallon kafar da suka bukaci sayen De Ligt ciki kuwa har da Barcelona da Manchester United dan wasan, da kan sa ya zabi Juventus.

De Ligt wanda ya bugawa Holland wasanni 15 ya kuma rattaba hannu kan kwantiragin biyan yuro miliyan 150 matukar ya bukaci rabuwa da Club din kafin karewar kwantiraginsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.