Isa ga babban shafi
Wasanni

Overmars ya shawarci Arsenal ta maye gurbin Ozil da Ziyech

Daraktan wasannin kungiyar Ajax Marc Overmars, ya shawarci tsohuwar kungiyarsa ta Arsenal, da ta maye gurbin dan wasanta Mesut Ozil da dan wasan gaba na kungiyar ta Ajax, Hakim Ziyech.

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil daga hagu tare da takwaransa na Ajax Hakim Ziyech.
Dan wasan Arsenal Mesut Ozil daga hagu tare da takwaransa na Ajax Hakim Ziyech. Yahoo Sport UK
Talla

Overmars, ya kara da bayyana matukar mamakin yadda har yanzu Arsenal ba ta nemi sayen Ziyech ba, duk kuwa da cewa a bayyane take, matashin dan wasan na Ajax ya yiwa Ozil zarra a fagen sarrfa kwallo.

Yayin kakar wasan da ta kare, Ziyech ya ci wa Ajax kwallaye 21, ya kuma taimaka wajen ci mata wasu 24.

Dakushewar bajintar Ozil a Arsenal bayan karbar jagorancinta da Umai Emery yayi, ya haifar da muhawara kan makomar dan wasan a kakar wasa ta bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.