rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kwallon Kafa Wasanni CAF

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ighalo na daf da lashe takalmin zinare

media
Dan wasan Najeriya Odion Ighalo. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Dan wasan tawagar super Eagles na Najeriya Odion Ighalo, ya kara damarsa ta lashe takalmin zinare a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta wannan shekarar da ake daf da karkarewa a Masar, bayan ya saka kwallo a ragar Tunisia a wasan neman tagulla tsakanin Najeriya daTunisia a jiya Laraba.


Dan wasan mai shekaru 30 da ke wasa a kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua ta kasar China ya saka kwallo daya tilo na wasan ne dakikoki 130 da fara zubin farko na wasan da ya gudana a filin wasa na Al Salam da ke birnin Alkahira.

Wannan kwallo, ita ce ta biyar da ya ci a gasar ta bana, kuma ta sa ya tsere wa twakwarorinsa Riyad Mahrez, Adam Ounas, Cedric Bakambu da Sadio Mane wadanda suke da kwallaye uku ko wanne.

Riyad Mahrez da Ounas na Algeria, da Sadio Mane na Senegal na da damar kara yawan kwallayen da suke da su a wasan karshe da za a fafata gobe Juma’a a filin wasa na kasa dake birnin Alkahira.